"Wadda Zai Gaje ni Manomi ne"
-Tsohon Gwamna Badaru
A yau kenan, bayan zagayen duba yadda ake gudanar da rabon kayan noman alkama karkashin shirin NAGS-AP na gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa...Mai girma gwamnan jihar Mallam Umar A. Namadi FCA ya ke zagayen duba tasa gonar alkamar; domin ganin yadda aiki ke gudana.
Akwai cibiyoyin rabon wannan kaya (Redemption center) da dama a faɗin jihar Jigawa musamman kananan hukumomi 22 da ake wannan shiri na bunƙasa aikin noman alkama a jihar Jigawa. Gwamnan ya ziyarci 6 daga cikin waɗannan cibiyoyin wadda su ka hada da Kiyawa, Jahun, Miga, Kafin Hausa, Auyo, Hadejia, Guri da Birniwa.
A zagayen da mai girma gwamnan ya ke, ya gane wa idonsa yadda rabon ke gudana a wadannan cibiyoyi tare da sake jan kunnen wannan jami'ai wajen ganin an rabawa manoman a kan lokaci da kuma tabbatar da yin adalci.