Gwamna Namadi Ya Halarci Bikin Yaye Matasa 250 Da Su Ka Samu Horo Na Musamman A Kan Gyara Tare Da Tona Burtsatse(famfon tuka-tuka) Wadda Ma'aikatar Samar Da Aikin Yi Da Dogaro Da Kai Ta Jiha Ta shirya (Jigawa Agency for Empowerment and Employment)
Matasan waɗanda su ka shafe sama da watanni uku su na karbar horo a cibiyoyin koyon sana'o'i guda bakwai da ake da su a faɗin jihar Jigawa; sun fito ne daga mazaɓun ƙananan hukumomi 27 da ke faɗin jihar Jigawa. Sannan a yanzu haka, akwai wasu na karɓar horo a wasu fannonin, su ma za a yi bikin yaye su tare da basu kayan aiki nan ba da daɗe wa ba; kamar yadda babban darakta na wannan cibiya Dr. Habib Ubale Yusuf ya bayyana a jawabinsa.
Kowane matashi daga cikin matasan da aka horas, an bashi akwatin kayan aiki ta yadda zai dogara da kansa wajen aiwatar da gyaran famfunan burtsatse cikin kauyuka da birane na ƙananan hukumominsu.
Mai girma gwamna Mallam Umar A. Namadi FCA, a yayin jawabinsa ya hori wadannan matasa da su yi amfani da wannan ilimi tare da kayan aiki da aka basu wajen gina kawunansu domin dogaro da kai, sannan ya yi ƙira da shugabannin ƙananan hukumomi wajen tabbatar da sun bawa kowane matashi daga cikin matasan 250 da sabon babur domin ƙarfafa musu gwiwa wajen zagayen yawon gyara tare da tona famfunan burtsatsen.
Gwamna Mallam Umar Namadi ya sake ƙira ga shugabannin ƙananna hukumomi, wajen bawa waɗannan matasa dukkan ayyukan gyaran famfo da za ana yi a fadin mazaɓu na ƙananan hukumomin, domin karfafarsu da kuma basu damar su ma su dauki wasu matasan da za su na taya su. Gwamnan ya sake jaddada muhimmancin ruwan sha ga al'umma, da kuma yadda buƙatuwar wannan masu gyaran famfon zai bayar da ayyukan yi a wannan lokaci.
Gwamna Namadi ya sake bayyana aniyar Gwamnatin jihar Jigawa na samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma na bayan fage; wadda dama ya na cikin ƙudurorin gwamnatin Jigawa guda goma sha biyu (12 points Agenda for greater Jigawa). Daga karshen jawabinsa, gwamnan ya sake jaddada wa al'umma cewar za a sake daukan matasa a kowace ƙaramar hukuma domin ɓude musu shagon sayar da kayan gyaran famfo, a cikin shirin gwamnatin jihar Jigawa na samar ta attajirai 150 cikin shekara guda kamar yadda ya yi alwashi ( We will create 150 millionaires in one year)
Mallam Garba Al-Hadejawy, FCAI, FIMC
Special Assistant to the Governor
(New Media)