ƘUDURORIN MAJALISAR ZARTASWA TA JIHAR JIGAWA

Jigawa New Media Office
0
 
A taron Majalisar Zartaswa ta jihar Jigawa na ranar Litinin (25/3/2024) an amince da ƙudurori kamar haka:
 
1. Majalisar Zartaswa ta duba Rahoton Kwamitin Tantance Rahoton Kwamitin Bincike akan Manyan Makarantun Koyar da Ayyukan Kiwon Lafiya na jiha, inda ta umarci Ofishin Babban Akanta na jiha da ya aiwatar da shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar tare da ɗaukar waɗannan matakai:

I. Sauke shugabannin Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Birnin Kudu da suka haɗa da Provost, Bursar da Registrar tare da umarnin su kai kansu Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.

II. An sauke daraktocin Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Babura daga muƙamansu kuma za su kai kansu Ma’aikatar Lafiya.

III. Daraktocin Birnin Kudu, Hadejia da Babura za su biya kuɗaɗen da suka bayar da ba’asi akansu.

IV. An sauke Provost, Bursar da Registrar na Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun daga muƙamansu sannan kuma za su kai kansu Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.

V. Provost na Kwalejin Kiwon Lafiya zai bayar da dalilai kan ɓacewar kuɗaɗen shiga na kwalejin da waɗanda aka samu daga gwamnati waɗanda ba a bayar da ba’asinsu ba.

VI. Dukkan jami’an da suke karɓar albashin da bai kamata su karɓa ba sannan kuma ba a makarantun suke aiki ba amma sunayensu suka kan jadawalin albashi na makarantun, za su mayar da kuɗin da suka karɓa wanda ba haƙƙinsu ba ne.

VII. Ma’aikatar Lafiya za ta sabunta gine-gine da kayan aiki a Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.

VIII. Ma’aikatar Lafiya za ta ɗauki ƙarin ma’aikata domin cike giɓin ƙarancin malamai a waɗannan makarantu biyu.

IX. Gwamnati za ta kafa Hukumomin Gudanarwa na waɗannan makarantu biyu.

X. Ma’aikatar Lafiya za ta ƙara kuɗin abinci na ɗaliban Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.

2. Samar da ƙarin rancen kuɗi ga JASCO domin sayen buhunan takin zamani 90,000

(motoci 150) na NPK don kakar noma ta shekarar 2024 wanda za a sayar ga al’ummar jihar Jigawa. Za a sayo takin naira Biliyan Biyu (N2,000,000,000.00).

3. Gina gidajen kwana na ma’aikatan Ungozoma guda 7 tare da zagaye su a ƙananan cibiyoyin kiwon lafiya na: Abaya PHC a Dutse, Koya PHC a Miga, Kanzan PHC a K/Hausa, Madachi PHC a Kirikasamma, Yar’ Sara PHC a Roni, Chakwaikaiwa PHC a Taura da kuma

Amanga PHC a Sule Tankarkar. Za a yi wannan aiki ne akan kuɗi N305,674,439.11.

4. Sabunta kwangilar samar da lantarki mai aiki da hasken rana (solar) a Babban Asibitin birnin Dutse daga naira N172,754,158.00 zuwa naira N252,849,395.50.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)