Gwamnatin jihar Jigawa ta ware Naira biliyan goma sha uku da miliyan ɗari huɗu da arba'in da biyar da dubu tamanin da takwas da naira ɗari biyar da kobo arba'in (N13,445,088,500.40) domin ƙarasa ayyukan wasu tituna guda goma 17 da aka fara su tun a gwmanatin da ta gabata.
Wannan ya na ƙunshe ne a cikin wani ƙuduri da kwamashinan ma'aikatar ayyuka da sufuri ta jiha ya gabatar a majalisar zartarwa ta jihar Jigawa a ranar 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2024.
Sabunta kwantiragin da ƙarin ƙuɗaɗen ya biyo bayan hauhawa tare da sauye-sauyen farashin kayan aiki da aka samu.
Ga Hanyoyin Kamar haka:
1. Gina titin Maigatari-Jobi- Kuka Tankiya-Dan Takore- Danbanki-Dangwanki-Danmakama Mekekiya-Maizuwo-Baruma- Bandakado-Lululu zuwa Unguwar Gawo-Babura.
2. Gina titin Shuwarin-Wurma-Chamo-Abaya-Isari.
3. Gina titin Girimbo-Gantsa Kauya-Sagu-Kwanar YayarinTukur Lelan Kuou-Kukuma-Sara.
4. Gyara lalataccen sashen titin Dutse-Baranda-Waza-Gambara.
5. Gina titin Sule Tankarkar-Amanga-Maitsamiya-Tsugudidi-Santarbi-Garin Alko.
6. Gyara lalataccen sashen titin Birnin kudu-Sundumina zuwa Kiyawa.
7. Gyaran lalataccen sashen titin Jahun zuwa Gujungu.
8. Gina titin Kwanar Kuka- Gasanya-Manaba-Kutugu- Tagadawal-Akurya zuwa Tata.
9. Gina titin Yelleman-Kaugama zuwa Kwanar Madana.
10. Gina titin Auyo - Kaffaddau zuwa Ayama.
11. Gyaran lalataccen sashen titin hanyar Auyo-Kafin Hausa.
12. Gyaran titin Darai- Gilima
13. Gyaran hanyar Hantsu-Miga-Dangyatin
14. Gyaran hanyar Kiyawa-Jahun
15. Gyaran hanyar Kwalam-Gilima-Majiya
16. Gyaran hanya tare da gina kwalbatoci garin Gudunya a kan hanyar kanya Baba-Yarkirya- Babura
17. Gyaran hanyar Birnin Kudu-Zazika
-Al-Hadejawy