Kalaman gwamna Namadi kenan a lokacin da ya karɓi bakuncin Ms. Aline Mugisho, shugabar tawagar ƙwararru daga cibiyar bunƙasa fasahar aikin gona da yaƙi da yunwa da talauci ta ƙasashen yankunan sahara "International Institute of Tropical Agriculture (IITA) a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
Shugabar tawagar ta fara da jawabi a kan irin ƙalubalen da noma ke fama da shi a ƙasashen Afirka da sauran ƙasashen da ke yankin sahara na rashin samar da wadatattun kayan aikin gona na zamani da sabbin dabarun ayyukan gona duk da irin gudunmawa da ayyukan yi na fannin noman ke samar mana. Haƙiƙa hakan ya jawo ci baya da da koma bayan tattalin arziki. Ta ku yi bayani kan yadda haɗin kai da jihar Jigawa zai taimaki matasa wajen samar da ayyukan yi da inganta aikin noma.
Cibiyar ta yi duba da irin qalubalen da harkar noman ta ke fuskanta, da yadda yunwa da fatara ke rarakar al'ummar da ke yankunan sahara, wannan ta sa suka fito da tsare-tsare da sabbin dabaru da zai samar da ayyuka na kai tsaye ga dimbin matasa a ƙalla 52,000, wadda ya amfanar da dama da mutane 200,000 saboda rawar da matsan za su iya taka wa wajen farfaɗo da tattalin arziki. Cibiyar ta shafe sama da shekaru 50 a wannan fanni, kuma suna da irin wannan shiri a sama da ƙasashe 134 a duniya.
"Mun fara da jihar Lagos, Kaduna da sauran jihohi, yanzu mun zo Jigawa. Shirin ba ya bukatar ilimi mai zurfi, ko wani dogon shiri. Mun ga irin wannan ci gaba a ƙasashen Cuba da Syria su ka samu a fannin da su ka fi kwarewa, yadda aka zamanantar da ayyukan gona, yadda ƙasashen su ka zama abin kwatance a fuskar noma na zamani da harkar lafiya. Kuma mun ga yadda aikin noman ya samar da ayyukan yi da waɗanda ke layin noman. Tun daga kan masu nomawa, masu sayar da kayan aikin gona, masu fidda kayan waje, da sauransu.
A jawabinsa, mai girma gwamna Mallam Umar A. Namadi, ya yabawa tawagar wanann cibiyar ta bunƙasa fasahar aikin gona yadda su ka zaɓi jihar ta Jigawa, daga cikin jihohin da za su ci gajiyar wannan shiri na horas da matasa a kan fasahar aikin gona ta zamani. Sannan ya bayar da misalin yadda mu ke da dimbin al'umma matasa a wannan ƙasa, waɗanda su ke jira gwamnatoci ko al'umma su taimake su, ya isa izina ga gwamnatocin wannan ƙasa da su ƙarfafi aikin gona. Sannan ya yabawa musu yadda su ka zo da sababbin tsare-tsare da zai tafi da zamanin da mu ke ciki.
"A matsayinmu na shugabanni ya zama wajibi a yi dukkan shirin da zai samar wa da waɗannan matasa abubuwan yi. Da yawa sun yi karatu, wasu bakinsu sakandire, wasu na da digiri da sauran fannonin karatu. Noma shi ne babban hanyar da zai samar da ayyuka da kowa da kowa matukar an inganta shi. Wannan shi ne hanya ɗaya tilo da zai inganta tattalin arzikin kasar nan, ya kuma karfafa darajar kudinmu
Wannan shiri na noma da Samar da ayyukan yi, ya na daga cikin manyan ƙudurorinmu 12 na gwamnatin jihar Jigawa. Domin a yanzu muna da cibiyoyin koyon sana'a guda 7 a jihar Jigawa. Wadda a ƙalla mun horas da matasa kimanin 4,000 a fannin sana'o'i daban-daban domin dogaro da kawunansu. Sannan muna da cibiyo guda 3 a fannin horo a ayyukan noma A yanzu haka muna shiri yi wa shirin ayyukan inganta noma na jihar Jigawa kwaskwarima, ta yadda zai yi dai-dai da zamani ya yi gogayya da sauran takwarorinsa na duniya. Don haka a shirye mu ke mu baku dukkan goyon baya wajen haɗa hannu domin wannan shiri ya tabbata, domin matasanmu su dogara da kawunansu.
Shirin inganta ayyukan gona na jihar Jigawa ya samar da shiri na musamman domin samar da ayyukan ga Malaman gona sama da 1,000, wadda za su wayar da kan manoma wajen sabbin tsare-tsarenmu, da kuma tsarin samar da attajiran manoma guda 1,1000 a jihar Jigawa"
-Mallam Garba Al-Hadejawy FIMC, FCAI
Special Assistant to the Governor
(New Media)
Thursday, 16th May, 2024