Gwamna Namadi Zai Samar Da Sahshen Jirgin Ɗaukar Kaya (Cargo Airport) A Filin Jirgin Sama Na Ƙasa Da Ƙasa Da Ke Dutse.

Jigawa New Media Office
0


A ƙoƙarinsa na farfaɗo tare da inganta tattalin arzikin Jigawa hanyar samar da sahihan hanyoyin kuɗaden shiga ga jihar, gwamna Malam Umar Namadi ya kammala shirin samar da sahshen jirgin ɗaukar kaya (Cargo Airport) a cikin filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da ke Dutse (Dutse Internstional Airport)

Hakan ya biyo bayan wani yunƙuri da gwamnan ya yi, na haɗa gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin jiragen sama ta kasa (Ministry of Aviation) da kuma hukumar kula da jiragen sama da ƙasa domin ganin an samu wata sahihihar hanya da za a dinga fita da kayan amfanin gona, dabbobi da sauran kayayyakin da ake samar da su a jihar Jigawa da ma sauran maƙwabtan jihohi zuwa ƙasahsen ketare.

Tuni jami'ai su ka zo daga Abuja domin duba wannan tashar jirgi ta Dutse tare da bayar da dukkan shawari a guraben da ta ke da buƙatar gyara da kuma kawo kayayyakin da ake buƙata kafin ɗaga likafar tashar.

Gwamna Namadi, a yayin mayar da jawabi ga tawagar jiya juma'a 25/10/2024, a ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Lawan daraktan bincike ta tsare-tsare na ma'aikatar kula da jiragen sama ta ƙasa, ya bayyana buƙatar da ake da akwai wajen ganin Jigawa ta shiga sahun jihohin da ke fitar da kaya zuwa kasashen waje. Duba da yadda Jigawa ita ce ta ɗaya a noman zoɓo, riɗi, ƙaro, gero da kuma shinkafa ga kuma albarkatun dabbobi da mu ke da su. Ya kamata a yanzu haka a ce waɗannan kaya an fara shigar da su kasuwannin duniya.

Bayan aike takardar neman wannan aiki da gwamnatin jihar Jigawa ta yi, zuwa ma'aikatar kula da jiragen sama ta ƙasa, gwama Namadi ya samu tattaunawa da ministan harkokin jiragen sama na ƙasa, wadda ya bashi tabbacin wannan aiki zai yiwu da ikon Allah. Gwamna Namadi ya bayyana shirin da gwamnatin Jigawa ta yi, na haɗa kai da kanfanunuwa a ƙasashen larabawa wajen safarar ɗanyen nama zuwa ƙasashen gabas ta tsakiya.

-Mallam Garba Al-Hadejawy FIMC, FCAI, FCIFC
Special Assistant to the Governor 
(New Media)
26/10/2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)