Gwamnatin Jihar Jigawa, a ƙarƙashin jagorancin Malam Umar A. Namadi FCA tana ƙoƙarin samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma inganta tattalin arziƙinta ta hanyar zuba jari a fannin samar da lantarki. A shekarar da ta gabata, da kuma wannan shekarar; gwamnati ta kulla yarjejeniya da kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO don samar da wutar lantarki daga hasken rana. Wannan shiri zai gina ƙananan tashoshin lantarki masu ƙarfin megawat 10 a garuruwa shida: Haɗejia, Dutse, Gumel, Kafin Hausa, Kazaure da Ringim, domin samar da wadatacciyar wutar lantarki a jihar.
A matsayin wani ɓangare na wannan yunƙuri, gwamnatin Jigawa ta ƙara hannun jarinta a KEDCO daga kaso 7.5% zuwa 10%. Haka kuma, a ƙarshen shekarar da ta gabata, gwamnatin ta saka Naira biliyan ɗaya daga cikin biliyan shida na hannun jari da yi shirin saka wa a kamfanin na KEDCO domin aiwatar da wannan shiri, wanda zai samar da hasken lantarki da kuma kuɗaɗen shiga ga jihar.
Saboda mahimmancin wannan fanni, Gwamna Namadi ya samar da Ma’aikatar Lantarki da Makamashi na Zamani (Ministry of Power and Renewable Energy), inda aka ɗaga matsayin mai ba da shawara kan harkokin lantarki zuwa mukamin kwamishina.
Bugu da ƙari, gwamnatin Jigawa ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin Carbon EuroPAA da Uyo Green domin rage hayakin da ke gurbata muhalli (carbon emissions). Wannan shiri zai ba da damar samun tallafin kuɗi daga shirin rage dumamar yanayi na duniya, wanda Najeriya ta ware dala biliyan 2.5 domin yaƙi da sauyin yanayi.
A tsakiyar shekarar da ta gabata, Gwamna Namadi ya jagoranci shirin dasa bishiyoyi miliyan 5.5 a garin Andaza, wanda ke ƙaramar hukumar Kiyawa, domin hana kwararowar hamada. Haka nan, gwamnatin Jigawa ta sauya fasalin tashoshin samar da ruwan sha sama da 200 daga amfani da fetur/gas zuwa amfani da hasken rana. Hakanan, fitilun tituna da dama an maye gurbinsu da fitilun hasken rana, ciki har da titunan Kiyawa da Haɗejia. Shirin sauya fasalin fitilun zai ci gaba, ta hanyar faɗaɗa zuwa sauran ƙananan hukumomin da ke jihar Jigawa.
A ranar 4 ga Fabrairu 2024, gwamnatin Jigawa ta haɗa kai da hukumar samar da lantarki a yankunan karkara (REA) domin samar da megawat 1,000 na wutar lantarki da zai amfanar da fiye da garuruwa 100. Wannan an tattauna shi ne a wani taro da aka gudanar a Abuja, wanda ya haɗa masu ruwa da tsaki a fannin makamashi, masu zuba jari da wakilan gwamnatoci.
Jihar Jigawa ta zama jiha ta farko a Arewacin Najeriya da ta fara shirin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, wanda hakan ke rage dogaro da wutar lantarki daga manyan cibiyoyin wutar ƙasa (national grid). Haka kuma, akwai wasu ayyukan lantarki da ake aiwatarwa a jihar, ciki har da tashar lantarki mai ƙarfin megawat 1,000 a Gwiwa, megawat 80 da kamfanin Nova Scotia ke ginawa, da kuma megawat 200 da kamfanin Cogen Energy ke aiwatarwa.
Dukkan waɗannan shirye-shirye idan sun kammala, za su kawo wa Jigawa ci gaba ta fuskar kuɗaɗen shiga, wadatacciyar wutar lantarki, bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma kare muhalli daga dumamar yanayi. Hakanan, zai ƙarfafa zuba hannun jari daga ciki da wajen jihar, wanda zai taimaka wajen ciyar da Jigawa gaba.
jigawanewmedia@gmail.com