Jigawa GalaxyITT ta zama cibiyar sadarwar tauraron Ɗan Adam ta farko a Afrika.
-Daga Abu Akhnas
Malam ya cika alƙawarin farfaɗo da GALAXY, yanzu haka ana kan kammala gyare-gyaren hukumar domin ci-gaba da amfanuwar mutanen wannan jiha, ko a kwanakin baya mai girma Gwamnan ya tabbatar da kafa wasu hukumomi guda biyar wanda ciki akwai hukuma mai lura harkokin sadarwa (ICT).
Wannan ya sanya jihar Jigawa ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta fara gudanar da shirin koyo daga nesa a shekarun da suka gabata domin kiyaye wannan matsayi Malam ya ja ɗamarar dawo da martabar wannan ma'aikata. Wanda wannan na cikin shirin gwamnatin Tarayyar Najeriya kafa Galaxy Backbone don gudanar da tsarin sadarwa na Intanet na(Internet Protocol IP-based Network) na ƙasa baki ɗaya don samar da hanyar sadarwa tare da sauran ayyukan more rayuwa ga dukkan ma'aikatun gwamnati, sassan da hukumomi (MDAs). Sake farfaɗo da wannan hukuma tamkar sake dawo da ƙarfin tattalin arziƙi ne a wannan jiha kama daga kuɗin shiga zuwa zuwa takaituwar fitar su don amfani da yanar gizo.
Idan ba a manta ba, a baya Maigirma Gwamna Malam Umar A Namadi ya ziyarci ofishin Galaxy da ke Abuja a ƙarshen inda ya tattauna da Manajan Darakta na GBB, Farfesa Muhammad Abubakar kan ɓangarorin haɗin gwiwa da kuma lalubo hanyoyin inganta harkar domin samun kuɗaɗen shiga da kuma taƙaita wahalar hanyoyin sadarwa na zamani. Ya kuma lashin takobin ci gaba da inganta kamfanin Galaxy Backbone domin tabbatar da gudanar da mulki ta hanyar yanar gizo, inganta samar da kuɗaɗen shiga da kuma bunƙasa fasahar sadarwa a jihar Jigawa.
Wanda wannan na cikin dalilan da yasa aka ƙirƙirar da shirin sadarwa na Broadband na jihar Jigawa ne saboda muradin gwamnatinsa na samun saurin bunkasar zamantakewa da tattalin arziki na matasan jihar da kuma gogayya da ƙasashen duniya ta fannin saye da sayarwa da kuma amfani da fasahar sadarwa.
Wannan yunƙuri zai saukaka harkokin kasuwanci na gwamnati, ilimi, horo da tsarin kiwon lafiya na jihar. An dai samar da kamfanin sadarwa na (Galaxy Information Technology and Telecommunication (GITT) a shekara ta 2000 a gwamnatin tsohon gwamna Alh. Ibrahim Sani Turaki gwamnatoci da dama sun alwashin dawo da hukumar a hayyacin ta amma hakan bai tabbata ba sai wannan karon ƙarƙashin digital governor Malam Umar A Namadi.
Masana harkokin sadarwa a baya kamar marigayi Malam Muhammad Auwal Albani Zaria, ya tabbatar da cewa wannan cibiyar ita kaɗai idan an inganta za ta iya kawowa Najeriya kaso mafi tsoka na kuɗin shiga ba wai Jigawa ba har cikin karatunsa mai taken INTERNET BAIWAR ALLAH yake cewa magani a gonar yaro.
Malam tabbatar da walwalar talaka ya zo!