Za a kashe sama da Naira biliyan goma sha huɗu da milyan goma sha huɗu (14.14bn) a fannin inganta aikin noma da tsaro na abinci (Agriculture and Food Security)
Kamar yadda kowa ya ga kamun ludayin wannan gwamnati ta Mallam Umar A. Namadi, ya san ta na bawa fannin noma gagarumin muhimmanci duba da yadda aka fidda da sabbin hanyoyi domin haɓaka harkokin noma.
Ko a watanni biyu da suka gabata, gwamnatin jihar Jigawan ta samar da tantan guda 54 domin tallafawa manya da kananan manomanmu na jihar Jigawa a dukkan kananan hukumomi 27 da ke fadin jihar nan.
Sannan an samar da takin zamani wadda aka sayar da shi ga manoma cikin farashi mai sauki, an kuma tabbatar da takin ya je hannun manoman.
Gwamnatin jihar Jigawa da hadin gwiwar gwamnatin tarayya ta samar da shirin noman alkama wadda za a noma sama da hekta dubu arba'in (40,000 hectres) a kananan hukumomi ashirin da biyu da ke jihar nan. Kuma tuni manoman sun fara karbar kayan aikin gona wadda aka bada shi kusan kyauta, domin tuni gwamantin ta dauki nauyin kaso saba'in da biyar na abin da aka bayar (ma'ana, dukkan manomin alkamar zai biya kaso ashirin da biyar ne cikin ɗari na kudin kayan da aka bashi)
Wadannan abubuwan kawai na cikin kwarya-kwaryar kasafin kudin bana ne (2023 Supplementary Budget) wadda aka ware biliyan arba'in da hudu (44bn). Idan Allah ya kai mu shekarar 2024 manoma za su sake yin dariya. Domin akwai tsare -tsare masu tarin yawa domin haɓaka harkokin aikin gona da tsaro na abinci.