KASAFIN KUDIN JIHAR JIGAWA NA SHEKARAR 2024:
Fannin lafiya zai ci kaso goma sha biyar bisa ɗari (15% Abuja Declaration) na adadin yawan kuɗaɗen da aka ware a kasafin kudin (298.14bn). Wadda ya haɗa da karasa wasu manyan ayyuka, dayan kayan aiki, daukar ma'aikata, ayyukan yau da kullum, gyare-gyaren manya da ƙananan asibitocin da suka samu matsala.
Gwamnatin da ta gabata ta gina asibitoci da dama, an daga darajar ƙananan asibitoci zuwa manya, an samar da asibitoci a dukkan mazaɓun da ke fadin jihar Jigawa.