GWAMNA NAMADI YA ƘADDAMAR DA RABON TALLAFIN JARIN N50,000 GA MUTANE 4,239

Jigawa New Media Office
0


Mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin jari na Naira 50,000 ga mutane 4,239 da ke fadin jihar Jigawa a karkashin shirin rage radadi ba cutar mai sarkewar numfashi (J-CARES) wadda ma'aikatar mata da walwalar jama'a tare hadin gwiwar ma'aikatar samar da ayyukan yi da rage radadi ta jaha su ka shirya.

A jawabinsa, mai girma gwamnan ya sake jaddada aniyarsa ta kudirin gwamnatin jihar Jigawa na rage radadi tare da samar wa al'umma hanyoyin dogaro da kawunansu ta yadda za a yaki talauci da zaman banza a tsakanin matasa. Sannan wannan tallafi na masu kananun sana'o'i guda 4,239 an yi shi bisa tsari tare da tabbatar da adalci wajen isar da sakon ga waɗanda suka cancanta; kuma an samar da katin ATM ne wadda ƙowanne daga cikin waɗanda za su amfana da wannan tallafi an buɗe masa asusun banki wadda kai tsaye zai cire kuɗinsa sannan ya ci gaba da amfani da wannan asusun wajen gudanar da kasuwancinsa ta hanyar da ya dace.

Gwamnan ya sake jaddada ƙudurin gwmanatin jiha wajen ƙirƙiro da sabbin hanyoyi wajen tallafawa al'ummar jiha. Wadda ko a gobe ma za a tallafawa masu buƙata ta musamman guda 1,000 da makamancin irin wannan tallafi. Sannan akwai tallafi na N50,000 ga mutane 28,000 wadda za a ƙaddamar shi nan ba da jimawa ba; kamar yadda a baya aka yi irin wannan tallafin ga mutane kusan 2,500.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Jigawa Engr. Aminu Usman Gumel, kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa; Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, sanata mai wakiltar Jigawa ta arewa masu gabas; Alhaji Babangida Hussaini Adamu, sakataren gwamnatin jihar Jigawa; Bala Ibrahim Mamsa, Dan majalisar tarayya mai wakiltar Masarautar Kazaure; Muhammad Mukhkar, Darakta janar na kamfen; Alhaji Lawan Ya'u Roni, shugaban jam'iyyar APC na jiha; Alhaji Aminu Sani Gumel, shugaban hukumar samar da ayyukan yi da rage raɗaɗi ta jihar Jigawa; Dr. Habibu Ubale.

-Mallam Garba Al-Hadejawy FCAI, FIMC

Mataimaki na musamman ga mai girma gwamnan jihar Jigawa a fannin sabbin kafafen sada zumunta.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)