GWANNA NAMADI YA ƘADDAMAR DA RABON TALLAFIN NAIRA 30,000 GA MASU BUƘATA TA MUSAMMAN GUDA 1,000

Jigawa New Media Office
0


Mai girma gwamnan jihar Jigawa ya ƙaddamar da rabon tallafin Naira 30,000 ga masu buƙata ta musamman 1,000 a jihar Jigawa.

Taron wadda ya gudana a ɗakin taro na "Manpower Development Institute (MDI" da ke babban birnin jihar Jigawa, Dutse; wadda ma'aikatar mata da walwalar jama'a tare da hadin gwiwar hukumar samar da aikin yi da dogaro da kai ta jiha su ka shirya.

Taron wadda ya ke shi ne na farko tun da aka kafa jihar Jigawa, ya tara masu buƙata ta musamman (Guragu, kurame, makafi da sauransu) daga ƙananan hukumomi 27 da ke fadin jihar Jigawa.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin wannan satin; kamar yadda a jiya 15 ga watan Janairu na shekarar 2024 mai girma gwamnan ya ƙaddamar da tallafin N50,000 ga masu ƙananan sana'o'i guda 4,239 da ke fadin wanann jiha. Haka a watanni baya gwamnatin jihar Jigawa ta tallafa wa mata 1,000 da jari na N50,000 da kuma matasa guda 1,500 da N50,000 kowanne.

A jawabinsa; mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi, ya sake jaddada ƙudurin gwmanatin jihar Jigawa na tallafawa dukkan rukunin al'umma tare da tafiya a kan doron ƙudurorin gwamnatinsa guda 12 (12 points Agenda).

Gwamnan ya umarci ma'aikatar mata da walwalar jama'a ta su gaggauta sabunta rejistar masu buƙata ta musamman domin ci gaba da biyansu kamar yadda gwamnatin jihar Jigawa ta yi doka a shekarar 2007. Sabunta rejistar zai bayar da damar ƙara yawan mabuƙatan, yawan ƙudin da sauya sunayen waɗanda su ka rasu.

Taron ya samu halartar manyan jigajigan gwamnati, wadda su ka hada da mataimakin gwamnan jiha, kakakin majalisar dokokin jiha, sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma'aikatan gidan gwmanatin jiha, shugaban jam'iyya ta jiha, kwamashinoni, da sauran mahalarta taron.

-Mallam Garba Al-Hadejawy, FCAI, FIMC

Mataimaki na musamman ga mai girma gwamnan jihar Jigawa a fannin sabbin kafafen sada zumunta.

16 ga watan Janairu na shekarar 2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)