GWAMNA NAMADI YA SHIRYA LIYAFAR BANKWANA GA ƊALIBAN JIHAR JIGAWA 194 MASU TAFIYA ƘASAR CYPRUS KARATUN LIKITANCI

Jigawa New Media Office
0

Domin nuna kulawa da karfafa gwiwa, mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA ya shirya gagarumin taron Liyafar cin abinci ga dalibai 194 yan asalin jihar Jigawa masu tafiya karatun likitanci zuwa kasar Cyprus da India. 184 daga ciki za su tafi jami'ar "Near East University,  Cyprus" sai guda 10 da za su tafi jami'ar "Integral University, India"

Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar Jigawa ta ware sama da naira sama da biliyan biyu  domin mayar da wannan dalibai zuwa kasar Cyprus don ci gaba da karatunsa.

Daliban waɗanda ke karatu a kasar Sudan kafin ɓarkewar yakin Basasa a kasar, sun samu irin wannan gata da kulawa daga gwamnatin jihar Jigawa wajen samo musu makaranta mai inganci a ƙasar Cyprus da India, wadda su na daga cikin manyan makarantu masu inganci a duniya.

Gwamna Namadi ya hori ɗaliban wajen mayar da hankali tare jajircewa don ganin sun samu abin da ya kai su wannan ƙasa, tare da zama wakilai nagari wadda jihar Jigawa za ta yi alfahari da su.

Taron ya samu halartar manyan jigajigan gwamnati wadda su ka hada da mataimakin gwamnan jiha, kakakin majalisar dokoki ta jiha, sakataren gwamnatin jiha, shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Jigawa, shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar Jigawa, shugaban ma'aikata na jiha, Kwamishinan ilimi mai zurfi, kwamashinan ilimi matakin farko, Kwamishinan lafiya, kwamashinar kudi, kwamashinan kasafin kudi da tsara tattalin arziki, sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha,  'yan majalissu na jihar, shugabannin ƙananan hukumomi masu bawa gwamna shawara, mataimakan gwamna na musamman, iyayen ɗalibai da sauran al'umma mahalarta taron.

Mallam Garba Al-Hadejawy FCAI, FIMC

Special Assistant to the Governor

(New Media)

January 29, 2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)