Noma Shi Ne Babbar Hanya Ɗaya Tilo da Za Ta Fidda Al'ummar Najeriya Daga Talaucin Da Ake Fama Da Shi

Jigawa New Media Office
0


Jawabin mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA lokacin da ya kaɓi tawaga i daga Bankin raya ƙasashen Afirka (African Development Bank) biyo bayan shirin noma alkama da kuma ziyarar babban ofishinsu da ke birnin Abidjan na ƙasar Ivory Coast.

Wannan ziyara ta biyo bayan shirin noman alkama na ƙasa ƙarƙashin shirin haɓaka noma na "National Agricultural Growth scheme" a tsagin "Agro-pocket Program" (NAGS-AP)

Tawagar babban bankin, a karkashin jagorancin Mr. Martins Fregene wadda shi ne shugaban wannan tawaga, ya yaba wa gwamnatin jihar Jigawa bisa namijin ƙoƙari da ta nuna a fannin noman alkama, wadda ya nuna ƙarasa a shekara mai zuwa za a iya bawa jihar Jigawa hekta dubu ɗari, maimakon dubu arba'in da aka bata a wannan lokaci. Sannan ya sake jaddada manufar bankin raya kasashen Afirka a cikin shirinsu na "Feed African Initiative", wadda zai yaƙi yunwa da fatara a ƙasashen Afirka. Wadda ya ƙunshi samar da abinci ta hanyar noman zamani.

Shugaba tawagar ya yaba yadda ya nuna jihar Jigawa kadai za ta iya samar da duk abin da ake buƙata a duk duniya a fannin noman alkama. Ganin yadda jihar ta zama abin kwatance, wadda a tarihin irin wannan shiri ba a taba samun jiha a duk cikin nahiyar Afirka a karon farko ta samu irin wannan nasara. Wakilan sun nuna yabawarsu ganin yadda su ka zagaya guraben da ake noman alkamar su ka ga yadda aka yi noma yadda ya kamata.

A nasa jawabin, mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA ya yaba wa gwamnan gwamnatin tarayya bisa ƙoƙarinta ƙarƙashin ma'aikatar noma da tsaro na abinci ta ƙasa, sannan ya yaba wa shugaban bankin raya kasashen Afirka, Dr. Akinwumu Adesina, bisa irin ƙoƙarinta na tallafawa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka a fannin noma. Gwamnan ya yaba da irin ƙokarin da jami'an bankin su ka yi wajen ganin shirin noman alkma na "Agro-pocket Program" (NAGS-AP) ya tabbata a jihar Jigawa. Ta yadda gwamnatin jiha tare da haɗin gwiwar bankin raya ƙasashen Afirka aka saukaƙa wa manoma wajen biya musu kusan kashi 75 na ƙudin kayan amfani gona da aka bayar. Kowane manomi zai biya kaso 25 ne kawai bisa ɗari na kuɗin abin da aka bashi.

Mai girma gwamnan ya sake ƙira da bankin raya kasashen Afirka da ya sake bawa jihar Jigawa dama wajen faɗaɗa shirin nomansu zuwa sauran fannonin ayyukan noman rani da damana. Gwamnan ya sake jaddada buƙatar gwamnatin jihar Jigawa kamar yadda ta nuna bajinta da kwazo a shirin noman alkama na bana, da a ƙara mata yawan faɗin hekta din da aka bayar zuwa 150,000; domin jihar Jigawa ta na da fadin albarkatun ƙasa da za a iya wannan aikin. Sannan ya nemi da a sake ɓullo da sabbin hanyoyin aikin gona na zamani. Gwamnan ya sake jaddada ƙudurorin gwamnatin jihar Jigawa cikin ƙudurori goma sha biyu na gwamnatin jihar Jigawa (12 Points Agenda for Greater Jigawa), ta yadda gwamnatin jihar Jigawa ta sabunta kasuwar duniya ta Maigatari (Maigatari Boarder Free Processing Zone), wadda za a dinga sarrafa zobo (Hibiscus and Sesame Fumigation centers).

Gwamnan ya sake bayyana manufar gwamnatin jihar Jigawa na shirin ƙinƙisar attajirai a fannin noman shinkafa na "Rice Millionaires Program" da kuma yadda aka faɗaɗa shirin noman kulosta (cluster farming) da ake yi a jihar Jigawa wadda a yanzu gwamnatin jihar Jigawa ta ɗauki aniyar farfaɗo da cibiyoyin binciken aikin gona ta jihar domin koya wa waɗannan matasa sabbin dabarun samar da iri na zamani. Ya bayyana yadda noma ya zama shi ne ke bayar da kashi 60 cikin 100 na gudunmawar haɓaka tattalin arziki a Najeriya; wadda ita ce hanya ɗaya tilo da za ta fidda al'ummar Najeriya daga talauci. Ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar Jigawa na ganin an yi bakin kokari wajen sauke dukkan da aka dora mata. Ta yadda gwamnatin jihar Jigawa ita ce ta farko wajen tilasta wa masu rike da madafun iko sanya hannu kan yarjejeniyar aiki (performance bond).

Mallam Garba Al-Hadejawy FCAI, FIMC

Special Assistant to the Governor

(New Media)

February 6, 2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)