Yadda Muka Sasanta Tsakanin Manoma Da Makiyaya Da Ba Sa Ga Miciji Da Juna – Gwamna Namadi

Jigawa New Media Office
0

 Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi FCA, ya bayyana yadda ya sasanta tsakanin manoma da makiyaya da ke rikici a karamar hukumar Guri dake jihar Jigawa.

 Gwamnan ya ce, an sanar da shi yadda wani shugaban Fulani ya zama ƙadangaren bakin tulun dake ke da hannu dumu-dumu wajen rura wutar rikici tsakanin ɓangarorin biyu, wadda har ya yi barazanar ɗaukan tsattsauran mataki akansa.

Gwamna Namadi ya ce, ɗaukan tsauraran matakai akan lamarin abu ne da ya zama wajibi domin ceto rayukan dubban mazauna yankin wadanda rikicin yankin yake rutsa wa da su.

 Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya halarci wani gagarumin biki da aka gudanar a ranar Lahadi a rigar Boɗala a karamar hukumar Guri domin murnar wanzuwar zaman lafiya a yankin.

 “Na gayyace shi mun zauna da shi (Lamiɗo Gide) kuma a gaban kwamishinan ‘yan sanda na faɗa masa cewa, dole ne ɗaya daga cikin biyu ya faru, ko dai ka bar zaman lafiya ya wanzu a wannan yanki, ko kuma in ba da umarnin harbe ka. Ashirye nake da na yi duk wata mai yuwuwa don ceto dubban rayukan alumma,” a cewar gwamna Namadi.

 Gwamnan wanda yake jawabi cike da annuri, ya ce an samu sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu bayan ƙulla yarjajjeniya da Lamiɗo Gide wanda da farko ya ke da kuskuren fahimtar zaman lafiya tsakanin al'umma.

 “Ba za a iya ƙididdige rawar da Lamiɗo Giɗe ya taka wajen wanzar da shirin wannan zaman lafiya ba. Yin adalci ga kowane bangare shi ne zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin bangarorin da ke rikici da juna. "Da na amince da batun da aka yi a baya game da Lamiɗo Gide na cewa ba zai taɓa barin zaman lafiya ya wanzu a wannan yanki ba, ba tare da na gayyace shi ba, da mun shiga cikin matsala har ya zuwa yanzu,” in ji gwamnan a wajen taron wadda shi ma Lamiɗo Gide ya halarta.
 Ya ja hankalin makiyayan ƴan asalin yankin da su sa ido game da karɓar baƙin mutane dake shigowa su cakuɗu da su.

 “Kada ku zura ido baƙin mutane su zo su ɓata zaman lafiya da muke da shi na tsawon shekaru.
 “Kada wanda ya bari wani baƙuwar fuska ya zauna ba tare da izinin Sarkin Hadejia ba,” in ji gwamna Namadi..

Ƙaramar hukumar Guri da yankin karamar hukumar Kirikasamma da ke makwabtaka da juna, yanki ne da ke da ƙasa mai albarkar noma da kiwo. Sai dai fafutikar neman mallakar wuraren dausayi ya haifar da munanan rigingimu tsakanin manoma da makiyaya shekara da shekaru. 

 Baya ga kiwo da noma, dajin na da halittu kusan nau'in tsuntsaye masu ƙaura aƙalla 378 daga yankunan Turai da Australia.

 A cewar mazauna yankin, jamian gidauniyar kare namun daji, da suka haɗar da8 Yarima Philip da Sarki Charles sun ziyarci yankin.
 Duk da cewa a tsawon shekarun da suka gabata yankunan biyu sun sha fama da rikicin manoma da makiyaya, amma ƙaurar da makiyayan ke yi a yankin ya ƙara ta’azzara rikicin, wanda ya yi sanadiyar laƙume rayukan mutane da dama.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)