GWAMNA NAMADI YA JAGORANCI TAWAGA TA MUSAMMAN ZUWA ƘASAR HABASHA KAN SHIRIN NOMAN ALKAMA:

Jigawa New Media Office
0

Gwamnan jhar Jigawa Mallam Umar Namadi, ya fara wata ziyarar gani da ido a ƙasar Habasha (Ethiopia) tareda ƙaƙƙarfar tawaga da suka haɗa da; manyan mataimaka na musamman kan al'amuran noma, jami'ai da ƙwararru daga ma'aikatar kula da harkokin aikin gona ta jihar Jigawa da ma dukkan masu ruwa da tsaki.
 
 Manufar ziyarar shine yin nazari dangane da shirin samar da Alkama na ƙasar Habasha, musayar ilmi tare da manyan jami'an aikin gona na ƙasar ta Habasha domin samar da sabbin dabaru a fannin.

 Kasancewar Alkama ita ce abinci na biyu a faɗin duniya da aka fi samarwa, tana taka muhimmiyar rawa wajen daƙile ƙalubalen samar da abinci a duniya. Habasha (Ethiopia) ta kasance babbar ƙasa a fannin noman alkama a nahiyar Afirka, wanda hakan ke nuna nasarorin da aka samu wajen ɗorewar noma da samar da albarkatun ƙasa.

 Ziyarar na da nufin cimma muhimman ƙudurori, da suka haɗar da: Tantance sashen noman alkama na ƙasar ta Habasha da aka cimma nasararsa. Gudanar da musayar ilmi kan shirin samar da alkama mafi inganci, da tunkarar ƙalubale dake tattare cikin shirin, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Habasha da Najeriya.
Gano tsare-tsare mai ɗorewa na tsarin noman alkama na ƙasar, fito da cigaba da ƙalubale da ake samu. Nazarin hanyoyin samar da kayayyaki mabambanta, da baje kolin ingantattun samfuri; noma don riba da saurasu

 A yayin ziyarar aikin ta kwanaki huɗu, tawagar jihar Jigawa za ta samu ilmi kan noman alkama a lokutan rani da damina.

 A halin yanzu, jihar Jigawa ita ce kan gaba wajen noman alkama a faɗin Najeriya, wanda ke bayar da gagarumar gudunmawa sosai ga fannin noma da samar da abinci, kuma ana sa ran rangadin zai buɗe wa jihar ƙofar damammaki tare da cimma wasu muhimman ƙudurori da za su taimaka wajen bunkasa noman alkama mai dorewa a jihar.

 Ziyarar ta jaddada ƙudirin gwamnatin gwamna Mallam Umar Namadi a jihar na binciko sabbin dabarun hanyoyin noma domin inganta samar da abinci da mayar da harkar noma don riba ga mafi yawan al’ummar jihar..

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)