Ƙungiyar Ƙula da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu da Jarirai ta Jihar Jigawa (JiMAF) ta jinjinawa Gwamna Namadi

Jigawa New Media Office
0
Ƙungiyar kula da lafiyar mata masu juna biyu da Jarirai ta Jihar Jigawa wato "Jigawa Newborn and Child Health Accountability Forum" (JiMAF) ta jinjinawa Gwamna Namadi bisa sahalewar saka Naira Biliyan Ɗaya (N1,000,000) a asusun kula da marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi na jihar Jigawa "Basic Health Care Provision Fund (BHCPF). Wadda za a yi shirin kula da lafiya da bayar da magani kyauta ga masu ƙaramin ƙarfi kimanin mutane 149,240 a faɗin mazaɓu 287 da ke jihar Jigawa.

Sun bayyana yadda wannan shirin zai taimaka wajen inganta kiwon lafiya musamman ga marasa galihu a jihar Jigawa.

Sannan sun sake yaba wa Gwamnan bisa sahalewar ware kaso 12.1% daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 na jihar Jigawa ga fannin lafiya.

Ƙungiyar ta sake gode wa gwamnatin jihar Jigawa bisa yunƙurinta na sake wa dokar inganta hukumar lafiya matakin farko ta jihar Jigawa fasali. Ta yadda za a yi gyare-gyare masu muhimmanci da za ta bada damar shigo da sabbin tsare-tsare da za su taimaka wajen inganta harkar kiwon lafiya matakin farko a faɗin jihar Jigawa.

-Al-Hadejawy 
25/04/2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)