GWAMNA NAMADI YA TAYA MA'AIKATAN JIHAR JIGAWA MURNAR RANAR MA'AIKATA TA DUNIYA.

Jigawa New Media Office
0

Mai girma gwamnan jihar Mallam Umar A. Namadi FCA ya taya ɗaukacin ma'aikatan jihar Jigawa murnar zagayowar ranar ma'aikata ta duniya.

Gwamnan wadda ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar Jigawa Engr. Aminu Usman Gumel, ya jinjinawa ma'aikatan bisa kokarinsu da jajircewarsu wajen ciyar da jihar Jigawa gaba da kuma tabbatar da ƙudurori 12 (12 points Agenda for Greater Jigawa) na gwamnatin jihar Jigawa. Taron ya gudana ne a filin taro na Mallam Aminu Kano da ke babban birnin jihar Jigawa Dutse.

Gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar Jigawa bisa  fiddo da tsare -tsare wajen inganta rayuwar ma'aikatan jihar Jigawa. Ta yadda ya shaida cewar gwamnati na sane da irin yanayi na matsin tattalin arziki da yadda a ke fama da wahala a Najeriya da ma duniya baki daya.

A jawabin na gwamnan, ya mayar da hankali kan yadda gwamnatin jihar Jigawa ta fito da shirin noma na ma'aikata, shagunan sauƙi, tare da saka Naira biliyan ɗaya a asusun yan fansho domin ci gaba da biyansu  haƙoƙinsu ba tare da samun tsaiko ba, da kuma shirin ƙaddamar da sabon tsarin ƙarin albashi na ma'aikata.

Dangane da sha'anin tantance ma'aikata, kamar yadda shugaban ƙungiyar ƙwadago ya faɗa, gwamnan ya basu tabbacin yadda shirin zai inganta rayuwar ma'aikatan da gobensu don ganin an samu tsari mai ɗorewa. Haka sauran kiraye-kiraye da shugabannin ƙwadagon su ka yi, dangane da inganta alawus da kuɗaɗen tafiye-tafiye da alawus na zaman mitin na ma'aikata; gwamnan ya yi alkawarin duba tare da yin abin da ya dace, wadda a yanzu haka akwai kwamatin da gwamnatin jihar Jigawa ta naɗa a ƙarkashin ofishin shugaban ma'aikata na jihar Jigawa kan yadda za a inganta waɗannan alawus na ma'aikata.

Kwamatin da gwamnatin jiha ta kafa kan sabon tsarin albashi na ma'aikata, sun aiko da rahotonsu, kuma gwamnatin Jigawa za ta yi duba domin tabbatar da tsari mafi inganci ha dukkan ma'aikatan Jigawa.

Tun a jawabinsa, shugaban ƙungiyar kwadago na jihar Jigawa comrade Sunusi Alasan, wadda shi ne ya jagoranci jawabi a madadin sauran kungiyoyin kwadago na jihar Jigawa, ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa tsare-tsare da ta fito da shi don inganta rayuwar ma'aikatan jihar Jigawa da kuma yadda gwamnatin ta saka kuɗi Naira biliyan biyu a asusun yan fansho, sannan ya yi ƙira ga gwamnatin jihar Jigawa ta yi duba wajen ganin an kammala aikin shigar da ma'aikatan jihar Jigawa cikin manhajar IPPMS ba tare da samun tasgaro ba. Shugaba ya kara ƙira ga gwamnatin jihar Jigawa wajen ganin an ƙara alawus na tafiye-tafiye ga ma'aikata, duba da yanayi tsada da hauhawar farashin kayayyaki.

Daga ƙarshe, mai girma gwamnan ya sake jaddada godiyarsa ga dukkan ma'aikatan, tare da addu'ar fatan alkhairi da kuma taya murna bisa zagayowar wannan rana mai muhimmanci. 

Taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnati, wadda su ka haɗa da shugaban ma'aikata na jihar Jigawa, Muhammad K. Dagaceri, shugaban jam'iyyar APC na jihar Jigawa, Alhaji Aminu Sani Gumel, kwamashinoni, masu bawa gwamna shawara, mataimaka na musamman, shugabannin ƙanannan hukumomi, shugabannin kungiyoyin kwadago na jiha da na ƙasa, tare da sauran al'umma.

-Mallam Garba Al-Hadejawy FCAI, FIMC 
Special Assistant to the Governor 
(New Media)
May 1st, 2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)