TSARABAR AMURKA: GWAMNATIN JIGAWA ZA TA SAMAR DA TARAKTOCIN NOMA 300

Jigawa New Media Office
0


A matsayin wani ɓangare na alfanun tafiyar Gwamna Mallam Umar Namadi zuwa ƙasar Amurka, a yanzu haka Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin guiwa da wasu manyan kamfanoni da suka yi fice a fannin dabarun bincike da samar da kayan aikin gona na zamani domin bunƙasa harkar noma a wannan jiha.

An ƙulla wannan yarjejeniyar haɗin guiwa ne a wani zaman tattaunawa da aka yi a birnin Washington DC  tsakanin tawagar ƙwararru daga Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Namadi da kuma wakilan shugabannin kamfanonin John Deere da Tata International.

Tattaunawar da ta gudana tsakanin ɓangarorin biyu ta ta’allaƙa ne kan yadda za a samar da kuma bunƙasa dabarun noma tare da shigar da matasa cikin harkar noma domin ganin an ɗaga matsayi da inganta rayuwar al’ummar jihar Jigawa ta hanyar noma.

Daga cikin kyawawan sakamakon da wannan tattaunawa ta haifar shine ƙuduri na haɗin guiwa da aka zartas na samar da wani shiri da a cikinsa za a sayo tantan ɗin noma guda 300 daga kamfanin ƙera taraktocin noma na Deere, wanda ba da daɗewa ba za a kawo su jihar Jigawa don cigaba da inganta harkar noma a jihar. Wannan zai taimaka matuƙa wajen bunƙasar samun amfanin gona mai kyau da inganci a tsakanin ƙananan manoma na wannan jiha.

A ƙarƙashin wannan shiri ana sa ran za a horas da matasa sama da 1,200 kan harkar kasuwancin sayarwa da ba da hayar kayan aikin gona da kuma sarrafawa tare da gyaran taraktoci da sauran na’urorin aikin da za a samar. Babbar manufar wannan shiri ita ce jawo matasa su shiga cikin harkar noma, wanda a yau ita ce hanyar samar da isasshen abinci da bunƙasar tattalin arziki a jiha da kuma ƙasa baki ɗaya.

Wannan kuwa wani ɓangare na manufofin da Gwamna Mallam Umar Namadi ya ƙudurci aiwatarwa don inganta fannin noma da sauran fannonin rayuwa a Jigawa da ya zayyana a cikin ƙudurori 12 na gwamnatinsa.

Da yake magana kan ƙulla wannan haɗin guiwa, Gwamna Namadi ya ƙara jaddada muhimmancin yin amfani da dabaru da kayan aikin gona na zamani tare da jawo matasa cikin harkar domin ta hakan ne za a tabbatar an inganta wannan fannin na noma a nan gaba. Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da ttallafawa manoma, musamman matasa da a yanzu suka farar ganin muhimmancin wannan fanni, ta hanyar samar da kayan aiki da dabarun noma na zamani don cigaban al’umma.

Da wannan haɗin guiwa da aka ƙulla da kamfanin John Deere, wanda fitaccen kamfani ne a duniya kan harkar noma ta zamani, da kuma takwaran kamfanin wato Tata International, jihar Jigawa ta kama hanyar kai wa tudun-mun-tsira ta fuskar noma na zamani da zai ɗaga matsayin rayuwar al’ummarta tare da bunƙasa tattalin arzikinsu.

-Government House Media Office 
02/05/2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)