A daren jiya asabat 04/05/2024, a taronta na shekara-shekara na liyafar cin abinci da karrama gwarazan shekara, tsangayar horas ta akantoci wato "Institute of chartered Accountants of Nigerian" (ICAN) ta karrama gogaggen akanta, kuma babban alaramma a wannan Tsangaya; mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA.
ICAN ta bayyana gwamna Namadi a matsayin "icon of Accountability index" saboda irin yabo da gwamnatin jihar Jigawa ta samu a wajen tsantsani da taka tsantsan da dukiyar al'umma; kamar yadda alqaluman tantance yadda ake kashe kudin gwamnati na jihohin Najeriya ya nuna. Sannan an ayyana jihar Jigawa a matsayin jihar da ta fi gabatar da tsararren kasafin tattalin arziki da ake bibiyarsa daki-daki wajen gudanar da shi ba tare da kauce wa kan abin da aka tsara ba.
Saboda wannan yabo da gwamna Namadi da gwamnatin jihar Jigawa ta samu, ICAN din za ta bude Tsangayar ƙyanƙyasa tare da horas da sabbin matasan akantoci masu taso wa, a jihar Jigawa a karon farko a duk faɗin Najeriya.
A wata ziyara da sabon shugaban Tsangayar ta ICAN Mr. Innocent Iweka Okwusa ya kawo jihar Jigawa a ranar 11/08/2023 domin taya murna da godiya ga gwmana Namadi, bisa yadda ya yi ƙoƙari wajen ɗora jihar Jigawan a kan turba mai ɗorewa a fannin tafikar da dukiyar al'umma. Sannan da naɗa da yawa daga cikin mabiyan wannan Tsangaya a manyan-manyan muƙamai a gwamnatin jihar Jigawa, waɗanda sun taimaka don ganin an samu tsari mai kyau wajen kashe kuɗaɗen al'umma.
A irin wannan taro na karrama wa da liyafar cin abinci da su ka saba gabatar da shi duk shekara; ana karrama fitattu daga cikin mambobinsu da suka yi rawar gani a matakin da su ke. Sannan su na karrama manyan kamfanuwa da su ka yi ficd a fannin gudanarwa ta kudi da tanadi.
Taron da ya gudana a babban ɗakin taro na Monarch Event Center da ke yankin Lekki a birnin Legas, ya samu halartar manyan jiga-jigai daga ciki da wajen ƙasar nan.
Mai girma gwamna Namadi ya samu rakiyar manya-manyan jami'an gwamnati, sanatoci, yan majalisar jiha da na tarayya, jagororin jam'iya, Kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomi, masu bawa gwamna shawara, mataimaka na musamman da sauran al'umma masoya da magoya bayan gwamna Namadi daga ciki da wajen jihar Jigawa.
-Mallam Garba Al-Hadejawy FCAI, FIMC
Special Assistant to the Governor
(New Media)
5 May, 2024