MANUFAR MANHAJAR BIYAN ALBASHI TA IPPMS

Jigawa New Media Office
0

A cikin watan Satumba, 2023 Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi FCA, ya kaddamar da Sabuwar Manhajar Biyan Albashi ta Jihar Jigawa wato INTEGRATED PAYROLL AND PERSONNEL MANAGEMENT SYSTEM (IPPMS) wacce zata taimaka wajen Samar da kyakkyawan tsari na biyan hakkokin Ma'aikatan Jahar nan.

Manufar Samar da wannan tsari na IPPMS shine saukaka biyan Albashi da sauran hakkokin Ma'aikata, ta bangaren da kowa zai amfana da Shirin ba tare da yawaitar korafe-korafe ba, wanda a karshe de Ma'aikatan ne zasu murna da farin ciki bayan sun gano alfanun wannan tsari.

Anyi wannan tantancewar ce ba don a rikewa wani albashinsa ba ko a koreshi daga aiki ba, anyi ne don inganta harkar Ma'aikata da yi musu karin Girma duk lokacin da ya kamata ai musu ba tare da fuskantar wasu kalubale na rasa takardu ko aiwa mutum alfarma a kaishi matakin da bai kaiba wanda daga baya azo anata samun matsaloli wanda ka iya jawowa mutum wani hukunci na daban ba.

Tsarin IPPMS tsari ne da kowa zai amfana don ya tanadar da kowanne Ma'aikaci zai dinga samun dukkan hakkokinsa akan lokaci ba tare da samun matsala ba, wanda hakan zai kai ga wanyewa lafiya a lokacin da mutum yazo yin retire daga aiki.

Tsarin shine zai datse yadda mutane suke wuce shekarun barin aikinsu su kara shekaru wai duk dan suci kudin Gwamnati, hakan matsala ne tunda bayan duk shekarun da suka kara dole sai an cire albashin da suke karba acikin kudin Fansho din mutum, cirewar munsan zai haifarwa da mutum matsala, mutum zai so ace bai wannan ha'inci na karin shekarun retire ba.

Tsarine da zaa dinga yiwa mutum promotion akai-akai duk lokacin da ya dace ba tare da wuce shekarun promotion baaiwa mutum ba, tunda ya samar da Kundin bayanan Ma'aikata da lokacin da ya dace kowa ya amfana da riba da romon aikin da yakeyi, ba tare da neman alfarma, hanya ko bayar da cin hanci don ai maka promotion ba.

Tsarine da zai kawar da cin hanci, rashawa da promotion din mutum bai cancanta ba, muna sane komai nisan lokaci zaa gano wannan ha'inci kuma a hukunta mutum. To a kaucewa wannan matsalar IPPMS hanyace da ba ruwanka da neman alfarma don ka samu hakkinka wanda a karshe fansho dinka bazai samu matsala ba.

Manhajar IPPMS ta tattara dukkan Kundin Ma'aikatan Jahar Jigawa, wanda hakan zai taimakawa Gwamnati na sanin adadin Ma'aikatan ta da biyansu hakkinsu akan lokaci ba tare da samun yan bogi ba, Manhajar itace kadai mafita ga kalubale da Ma'aikata suke fuskanta na samun hakkokinsu, hakan bazai kara faruwa ba tunda ga maganin kowacce matsala ta samu.

Duk wanda baiga albashinsa ba yayi hakuri kowa zai gane, baya ga Gwamna Namadi ya bayar da umarnin biyan kowa da tsohon tsari tare da cigaba da gyara yan matsalolin da aka samu a tsarin na IPPMS, InshaAllah Alkhairi ne ga dukkan Ma'aikatan Jahar Jigawa wannan sabon tsarin, mude mika kyakkyawan zato da addua a kowanne lokacin kan ya dora mana Shugabannin mu kan dede da karesu.

Amb. Muhammad Salisu Seeker Dutse. 
SSA Students Affairs to Jigawa State Governor. 
3rd May, 2024.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)