SAKAMAKON TARON MAJALISAR ZARTARWA TA JIHAR JIGAWA NA YAU LITININ UKU GA WATAN SHIDA NA SHEKARAR DUBU BIYU DA ASHIRIN DA HUDU

Jigawa New Media Office
0

1)    Majalisar ta gudanar da zaman ta bisa jagorancin gwamna Malam Umar Namadi tare da chimma kudirori kamar haka.

2)    Majalisar ta amince da bada kudi kusan naira miliyan dubu biyu domin sayo kayan abinci wadanda za a siyar a sabbin shagunan rage radadin tattalin arziki da hauhawar farashin wato palliative shops a dukkannin mazabu dari biyu da tamanin da bakwai da ke fadin jahar nan.

2a) Kudin ya kunshi wanda za’a bugo Katina cirar kudi wato ATM da naurar aminciwa da cire kudi wato POS na musamman wainda za ayi amfani da shi a shagunan.

2b) Hakan na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin wadata jiha da abinci da rage yunwa da talauci da bunkasar tattalin arziki da kuma samar daaikin yi.

2c) Majalisar ta amince da kafa kwamiti mai wakilai goma da zai gudanar da bincike da bada shawarar yadda za a sami nasarar aiwatar da shirin.

2d) Kwamitin na bisa jagorancin shugaban ma’aikata na jihar a matsayin shugaba yayin da shugaban ma’aikata a gidan gwamnati zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran wakilan kwamitin sune kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman da kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi dana kasuwanci dana yada labarai da babban akanta na jiha. Da babban Daraktan hukumar samar da ayyukan yi ga matasa da babban sakatare na musamman a ofishin gwamna da kuma babban mai taimakawa gwamna na musamman kan fasahar sadarwar zamani da bunkasa tattalin arziki.

Anbawa kwamitn ka’idojin gudanar da aikin sa da kuma lokacin gabatar da rahoton sa ga majalisar ta yadda za a samu nasarar aiwatar da shirin,

3a) A lokacin zaman majalisar gwamnar jihar malam Umar Namadi ya sa hannu kan wasu sabbi da kuma dokokin da aka yiwa gyaran fuska  guda bakwai kamar haka

3b) Dokar da ta kafa hukumar kula da makarantun sikandire mai lamba ta uku ta shekarar 2024

3c) Dokar da ta kafa hukumar fasahar sadarwa ta zamani da bunkasa tattalin arziki.

3d) Da gyara dokar kananan hukumomi mai lamba ta shida ta 2024

3e) da gyara dokar hukumar zabe ta jiha mai zaman kanta mai lamba ta daya

3f) Da dokar kwaryakwaryan kasafin kudi ta kananan hukumomin jihar nan.

3g) Da dokar da ta kafa hukumar yiwa mazauna jihar nan rajista

Haka zalika a yau ne gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya sa hannu kan dokar kwarya kwaryan kasafin kudi na naira milyan dubu tamanin da biyar da miliyan dari hudu da goma.

Za ayi amfani da adadin kudin  ne wajen kammala wasu manyan aiyuka a kusan kashi chasain da daya na ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jiha.

SANARWA DAGA KWAMISHINAN MAA’KATAR YADA LABARAI, MATASA, DA WASANNI DA AL’ADU NA JIHA SAGIR MUSA AHMED

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)