- Abin da ba a taɓa yi ba a tarihin jihar Jigawa.
Tun bayan zamansa gwamnan jihar Jigawa daga cikin abubuwan farko da ya fara yi shi ne kafa kwamatin da zai binciki matsalar da ta addabi harkar biyan haƙƙoƙin ma'aikatan da su ka kammala aiki (Retirees), saboda abin ya ta'azzara, mutane da dama sun shiga cikin matsala.
Daga cikin matsalolin da kwamatin su ka binciko shi ne akwai ƙarancin ma'aikatan gwamnati da za su ci gaba da bayar da gudunmawa cikin asusun, domin asusun fansho kudi ne ake juya shi ta hanyar zuba jari da kadarori, wadda da ribar ne ake biyan fansho da giratuti.
Ƙwararru da dama sun bada shawari a kan yadda za a farfaɗo da asusun.Amma mai girma gwamna ya ɗauki tsagin tausayi da jin ƙai...
Malamin gwamna ya bada umarnin ɗaukar sama da matasa 6,000 aiki na din-din-din. Ya kuma umarci da a ɗauki kuɗi daga asusun gwamnatin jiha a saka (aro) a asusun fanshon domin a biya jama'a hakkinsu. Wadda a ka'ida asusun ne dole zai biya su. Amma gwamna ba zai iya jurar ganin dattawan da suka bautawa jiharsu na tsawon shekaru 35 wasu ma sun mutu a lokacin aiki, amma a ce suna ta faɗi tashi wajen neman hakkinsu.
Wanda bai san tsarin harkar fansho ba, sai ya ɗauka da ganggan aka yi jinkirin biyan 'yan fanshon haƙƙoƙinsu, kuma gwmanati ta na can tana wasu ayyukan na maƙudan nairori 😅. Shi kuɗin fansho asusu ne mai zaman kansa wadda ya ke daban da asusun gwamnatin jiha. Ta yadda ba wadda ya isa ya taɓa wannan kuɗin ko ya ke da ikon taɓa shi ko yin wani aiki da shi wadda ba na fanshon ba. Akwai tsaro mai karfi a kansa a ƙarƙashin hukumar PENCOM ta ƙasa.
Yanzu shekaru biyu kenan mai girma gwamna ya na wannan namijin ƙoƙarin wajen ganin ya rufe wannan wawakeken giɓin da gwamnatocin baya su ka bari na rashin ɗaukan wadatattun ma'aikatan da za su bada gudunmawa wajen farfaɗo da asusun. Gudunmawar da ma'aikata za su bayar ita ce; saka kason da ake cira daga albashinsu duk wata, da kuma kason da gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi ke saka wa (adashen gata). Wadda dole sai ma'aikatan dindindin ne ke bayar da wannan kaso da za a tara a zuba hannun jari ana juya shi. Barin ma'aikata aiki ba tare da an dauki sabbi ba, shi ne kawo zaizayewar yawan kuɗin da ke cikin asusun, wadda yawansu bai kai a sallami waɗanda ke barin aikin ba.
©Al-Haɗejawy