GWAMNA NAMADI YA JAGORANCI TAWAGAR ƘWARARRU ZUWA TARON ƘOLIN TSARIN ABINCI NA AFIRKA, A BIRNIN KIGALI NA ƘASAR RWANDA:

Jigawa New Media Office
0


Mai gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi ne ke jagorantar tawagar Jihar Jigawa a taron shekara-shekara na Tsarin Abinci na Afirka na shekarar 2024, wanda zai fara a ranar litinin a Kigali, Rwanda. Halartar gwamnan a taron na nuna ƙudirin Jihar Jigawa na canza harkokin noma, samun cin gashin kai wajen samar da abinci, da kuma haska Jigawa a matsayin abin koyi ga sauran jihohin Najeriya.

Taken taron na bana shi ne "Kirkira, Ƙaruwa, da Haɓakawa: Samar da Sauyin Tsarin Abinci a cikin Shirin Fasahar Zamani da Sauyin Yanayi," wanda aka shirya zai gudana daga ranar 2 zuwa 6 ga Satumba, zai tattaro muhimman masu ruwa da tsaki don tattauna makomar tsarin abinci na Afirka.

Gwamna Namadi zai gabatar da jawabi na musamman a taron, inda zai bayyana dabarun Jihar Jigawa da nasarorin da aka samu wajen cimma cin gashin kai a wajen abinci da dogaro da kai a fannin noma.

Tawagar Jihar Jigawa za ta halarci zauren tattaunawa na masu ruwa da tsaki don haskaka shirin  "Rice Millionaires Project" na jihar da rawar da ya ke takawa wajen taimakawa tsaron abinci na ƙasa, da kuma inganta samuwar takin zamani, tare da nuna sabbin hanyoyin da Jigawa ta ɓullo da su don magance wannan ƙalubale.

Tawagar za ta samu damar gana wa da jami'an gwamnati, abokan hulɗa, da masu zuba jari na bangaren kamfanoni  masu zaman kansu domin tattauna shirin haɗin gwiwa da kuma janyo masu zuba jari a ɓangaren noma domin bunƙasa fannin noma a jihar Jigawa.

Kasancewar noma shi ne ginshiƙin tattalin arziƙin Jihar Jigawa, yana daga cikin na gaba-gaba a daftarin manufofi guda 12 na Gwamna Namadi. Muhimman ayyuka a cikin wannan tsari sun haɗa da "Rice Millionaires Project," "Wheat Project," da kuma tsarin samar da cibiyoyi na musamman na sarrafa amfanin gona (SAPZs), domin tabbatar da juyinjuya hali a fannin noma.

Da yake jawabi kan halartar Jihar Jigawa a taron, Gwamna Namadi ya bayyana cewa: “Jihar Jigawa tana da burin cimma cin gashin kai wajen samar da tsaro na abinci ta hanyar samar da tsare-tsare masu inganci a fannin noma mai dorewa. Muna shirye-shiryen yin aiki tare da abokan hulɗa da masu zuba hannun jari domin su shigo a dama da su a ɓangaren noma da kuma bayar da dukkan gudunmawa ga samar da tsaron abinci a Afrika. Jihar Jigawa jiha ce mai albarkatun ƙasar noma, don haka muna gayyatar al'umma daga ko ina a faɗin duniya domin haɗa hannu  wajen inganta harkar  noma saboda samun makoma mai kyau ga mutanenmu na nahiyar Afirka."

Taron Kolin Tsarin Abinci na Afrika shine babban dandalin duniya na aikin gona da tsarin abinci na Afrika, yana tattaro masu ruwa da tsaki don tattaunawa da ƙara wa juna sani domin inganta tare da haɓaka tsarin tsaro na abinci a Afrika. Taken taron na wannan shekara yana nuna rawar da matasa, mata, kirkire-kirkire, da fasahohin zamani  za su taka wajen samun canji zuwa tsarin abinci mai ɗorewa, daidaito, a cikin kyakkyawan yanayi.

Gwamna Namadi ya samu rakiyar  tawagar kwararru;  wadda su ka haɗa da kwamahsinan lantarki da makamashin zamani na jihar Jigawa, ƙwararren mai bada shawara fannin noma, da ƙwararren mai bada shawara a fannin fasahar zamani,  da kuma mai ba da shawara kan harkokin gwamnatoci.

-Mallam Garba Al-Hadejawy FIMC, FCAI, FCIFC
Special Assistant to the Governor 
(New Media)

For 

Hamisu Gumel 
Chief Press Secretary to the Governor 
 Of Jigawa state
September 2, 2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)