TSARABA DAGA BIRNIN KIGALI, NA ƘASAR RUWANDA

Jigawa New Media Office
0


Taron tsarin abinci na Afrika wadda aka gudanar a birnin Kigali na ƙasar Rwanda daga ranar 2 zuwa 6 ga watan satumbar wannan shekarar ya samu halartar mai girma gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar A. Namadi FCA. Taron ya mayar da hankali ne kan kirkire, kirkire, zamanantar wa tare da fidda tsare-tsare a kan inganta aikin gona. Musamman duba da yadda ake samun sauye-sauye a kan canjin yanayi, fasahar sadarwa da sabbin dabarun aikin noma da za su tallafawa wajen tabbatar da juyin-juya hali a fannin noma da samar da tsaro na abinci a ƙasashen Africa. Babban manufar taron shi ne, a auna tare da yin nazari a kan irin nasarorin da aka samu ya fuskar aikin noma da kuma ɗaukar ɗamba wajen ganin an faɗaɗa harkar.

Taron tsarin abinci na Afrika, babban taro ne da a ke gudanar da shi duk shekara a kan inganta aikin noma da tabbatar da tsaron abinci a Afrika. A wannan shekarar, taron ya bayyana manufar Afrika a kan harkar noma da tsarin abinci ta hanyar bajekolin fasahoshi, kirkire-kirkire, sabbin hanyoyin aikin noma, da sabbin fasahoshi da za su sauya fasalin tsarin aikin noma a ƙasashen Afrika, wadda kai tsaye za su yi tasiri wajen samar da ayyukan yi ga dubban matasa maza da mata.

Tawagar mutane biyar da su ka wakilci gwamnatin jihar Jigawa a taron na bana a ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, ya haɗa da manyan jami'an gwmanati wadda su ke taka rawa a fannin inganta aikin noma da zamannatanr da shi, shirin fasahar zamani da kuma fannin lantarki da makamashin zamani wadda su na cikin dirka ta 7 a shirin raya muradun ƙarni, wadda ya yi ƙira ga samar da lantarki mai ɗorewa nan da shekara ta 2030. Manufar taron ta yi muwafaqa da manufofin gwamnatin jihar Jigawa guda 12 wadda ke ƙunshi a cikin daftarin manufofin .

Halartar jami'an gwamnatin jihar Jigawa a wannan taron, ba ƙaramin gagarumin tasiri zai kawo ba wajen samun sauye-sauye a fannin noma a jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya. Domin da jihar Jigawa ta ta samu halartar wannan taro mai tarun alfanu ba, da ƙasar Najeriya ta yi babbar asara, domin jihar Jigawa a kan gwadaben samar da kaso 25 bisa 100 na yawan abincin da ake buƙata a faɗin ƙasa.

Jihar Jigawa, a ƙarƙashin mulkin gwamna Namadi, ta faɗaɗa shirin noman alkama, noman zoɓo, noman riɗi, shinkafa, ƙaro da sauransu wadda suna da matukar muhimmanci wajen ɗora Najeriya a kan turbar samun tsaro na abinci da haɓaka tattalin arziki. A shekarar da ta gabata, jihar Jigawa ta ƙaddamar da gagarumin shirin noman alkama, wadda gwamnatin jihar Jigawa ta noma sama da kadada 55,000 cikin kadada 100,000 da gwamnatin tarayya ta ware domin shirin noman alkama na ƙasa a ƙarƙashin shirin samar da wadataccen abinci na gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A wani babban zauren tattaunawa da aka gabatar a taron, gwamna Namadi na daga cikin manyan masu tattaunawa a kan tsare-tsaren hukumar bunƙasa tattalin arzikin ƙasahen yammacin Afirka (ECOWAS). Tsare-tsaren da ya mayar da hankali wajen samun mafita mai ɗore wa a fannin aikin noma. Tattaunawar da mayar da hankali kan rawar da kungiyar ECOWAS za ta taka a kan tsare-tsaren gwamnatoci a kan aikin gona.

Waɗada su ka tattauna a zauren sun haɗa da Dr. Henry Musa Kpaka, PhD, ministan aikin gona na ƙasar Saliyo, Mr. Dominique Dedegbe, shugaban sashen kwararru tare da bibiyar shirin samar da tsaro na abinci a ma'aikatar noma ta jihar Benin, George Boahen, ƙwararran mai bada shawara a ma'aikatar noma da tsaro na abinci na ƙasar Ghana, sa kuma Me. Abdoulaye Traore, daraktan kanana da matsakaitan kamfanonin sarrafa amfanin gona a ma'aikatar noma ta ƙasar Cote d'voire. Mrs. Binta Toure Ndoye ita ce ta jagoranci zauren tattaunawar.

A wurin taron, mai girma Gwamna Namadi ya gana da wakilan bankin raya ƙasashen Afrika (AfDB) a ƙarƙashin jagorancin Dr. Martin Fregene, daraktan kula da fannin noma na bankin. Tattaunawar tasu ta mayar da hankali zamanantar da aikin noma domin riba a jihar Jigawa domin tabbatar da wadatatuwar kayan aiki ga ƙananan manoma.

Bankin na AfDB ya yi alkawarin tallafawa jihar Jigawa a fannin noma da fasahar zamani ta yadda za a bunƙasa harkar noman wajen samar da ingantaccen iri da takin zamani da injinan noma na zamani wadda kai tsaye suna da tasiri wajen samun wadatuwar kayan da ake noma wa da za su samu fice a kasuwannin duniya.

Manyan matakan da aka ɗauka wajen tabbatuwar shirin (KPIs) sun haɗa da rejistar manoma miliyan 2 da sanya sunayensu a cikin manhajar adana bayanai wadda aka ɗauki hoton katin shadairsu ta dan kasa, lambar asusun banki, bayanai gona da girmanta da kuma tsarin noma na kulosta. Shirin ya sake haɗa wa ɗaukar hoton taswirar gonakai sama da kadada miliyan 3, wadda aka shirya bayar da takardun shaidar mallaka ga manoman. Da kuma shirin sada manoma da kwararru da kuma yan kasuwa ta hanyar amfani da kafofin zamani da zai bawa manoman damar tallatawa da sayar da amfanin gonarsu a faɗin duniya.

A rana ta uku a taron, mai girma Gwamna Namadi ya halarci taro na sassa da dama inda ya yi bayanai sosai a kan irin dabarun da za a yi amfani da su waje kawo sauye-sauye a fannin noma. Ya kuma bude kofar jihar Jigawa wajen haɗa gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki ta fuskar musayar fasaha da ƙara wa juna sani domin tunkarar matsalolin sauyin yanayi wadda su ka zama kandagarki a fannin ci gaban noma. Don haka Jigawa a shirye ta ke ta haɗa gwiwa da gwamnatoci da kamfanunuwa masu zaman kansu domin samun nasara a fannin noma.

Gwamna Namadi ya halarci zaman na musamman da gidauniyar Bill and Melinda Gates da kuma wakilai daga kungiyar ECOWAS domin tattaunaw batun zamanantar da aikin gona da tallafawa ƙananan manoma wadda su ne babbar dirka wajen samar da tsaron abinci. Daga karshe ya halarci liyafar cin abinci wadda aka bayyana daftarin manufofin noma na ƙasar Saliyo, saannan ya gabatar da jawabin rufe taro. A tare da shi akwai Gwamna Umo Eno na jihar Cross Rivers. Sannan gwamna Namadi ya gana da tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan a can Kigali, a yayin da suka tattauna muhimman batutuwa da su ka shafi ci gaban ƙasa da al'amuran duniya. Sannan ya gana da Joseph Nsengimana, shugaban cibiyar Fasaha da ƙirƙira na gidauniyar MasterCard Foundation.

Tawagar ta jihar Jigawa sun samo hanyoyi muhimmai wajen faɗaɗa alaƙar jihar Jigawa a fannin kawo sabbin sauye-sauye a fannin ilimi, fasahar noma, gina matasa, da cigaban ƙanana da matsakaitan masana'antu. "Kullum burinmu shi ne mayar da hankali a kan kawo sauye-sauye da za haɓaka Jihar Jigawa ta fannin tsaro na abinci, fasahar zamani, inganta ilimi da kuma kawo matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta"
-inji gwanma Namadi.

A ranar ƙarshe, gwamna Namadi ya jagoranci tawagar jihar Jigawa zuwa cibiyar inganta  sahe ilimi ta kasar Rwanda wato "RwandaEquip". A yayin da shugaba cibiyar NewGlobe, Jay Kimmelman ya gabatar da wani bincike da suka gabatar a kan matsalolin ilimi a jihar Jigawa, da kuma fatan za a ɗabbaka irin ayyukan da wannan cibiyar ta ke a jihar Jigawa.

Gwamna Namadi ya yi wani zama na haɗaka tare da shugaban ƙungiyar fafutuka a kan sha'anin noma a Afurka wato "Alliance for Green Revolution in Africa (AGRA). Sun tattauna domin ganin jihar Jigawa ta shiga cikin jerin  jihohin da ke cin moriyar shirin na AGRA. Shugabannin na AGRA sun bayyana sha'awarsu wajen irin yadda jihar Jigawa ta fito da sabbin tsare-tsare a fannin noma , sun kuma yi alƙawari tallafawa jihar Jigawan a fannin inganta aikin noma wadda kai tsaye zai shafi ƙananan manoma. 

Sannan ya yi ganawa ta musamman da Farfesa Catherine L. Nakalembe, shugabar cibiyar bincike ta NASA a fannin aikin bincike a aikin noma. Domin tattauna yadda za a magance matsalolin ambaliyar ruwa da fari da ke fama da shi a sakamakon sauyin yanayi. Ta yi alkawarin tallafawa jihar Jigawa da kuma bayar da ingantattun bayanai da ake samowa ta hanyar amfani da tauraron ɗan adam, wadda zai taimaka matuƙa wajen magance matsalolin.

Gwamnan ya halarci bikin rufe taron samar da tsarin abinci na Afrika na shekarar 2023 tare da manyan shugabannin ƙasashe da masu ruwa da tsaki a fannin noma da fasahar zamani tare da jami'an diflomasiyya da ƙasashe da dama wadda su ka haɗa da mataimakiyar sakataren majalisar ɗinkin duniya, Amina J. Mohammed tare da firam ministan ƙasar Ruwanda. Taron ya mayar da hankali a kan haɗin gwiwa wajen fiddo da sabbin fasaha domin magance matsalar ƙarancin abinci a duk duniya.

Bayan kammala bikin rufe wa, gwamna Namadi ya gana da Ms. Sofia Boly, shugabar cibiyar kawo sauyi a fannin noma wato "African Agricultural Transformation Initiative (AATI), domin tsada yadda za a samar da cibiyar hukumar a jihar Jigawa kamar yadda aka da su a ƙasar Tanzaniya da Saliyo domin tabbatar da muradun cibiyar na ganin an inganta aikin noma da yaƙi da fatara.

A wajen taron, gwamna Namadi ya samu dimbin yabo tare da jawo hankalin manya-manyan shugabanni na duniya, masu ruwa da tsaki da masu zuba hannun jari. Kuma sun nuna sha'awarsu da haɗa hannu da jihar Jigawa ganin yadda sauye-sauyen da ake samu ya ƙayatar da su.

Shugabannin bankin raya ƙasahsen Afrika (African Development Bank) ya jinjinawa jihar Jigawa tare da yin zama na musamman na tawagar ta Jigawa don sake saurarar irin abubuwa da ya ji gwamna Namadi ya bayyana. Sun kuma nuna sha'awarsu wajen haɗa hannu da Jigawa.

Farfesa Sule Ochai, ya bayyana cewar, noma shi ne babbar hanya ɗaya da Jigawa za ta karfafa da  zai haɓaka dukkan sassa da su ke zama ma'aunin ci gaba. Ya ce domin magance matsalolin rashin aikin yi ga matasa a Najeriya, dole ne a tashi a tsaye a ƙarfawa matasan gwiwa wajen shiga harkokin noma domin riba. Ya kuma jinjina wa gwamna Namadi da irin namijin ƙoƙarin da ya ke a jihar Jigawa.

-Mallam Garba Al-Hadejawy FIMC, FCAI, FCIFC
Special Assistant to the Governor 
(New Media)

For 

Hamisu Gumel 
Chief Press Secretary to the Jigawa state Governor 
07/09/2024

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)