Gwamna Namadi: Lalacewar Gine-Ginen Makarantu, Kuɗin ilimi na Haɗaka (UBEC/ SUBEB matching funding) Zama na musamman da Shugabar Hukumar Ilimin bai ɗaya ta ƙasa (UBEC):

Jigawa New Media Office
0

 Da farko dai muna miƙa godiya ga masu ɗauko hotunan makarantun da suka lalace a wasu yankuna na jihar Jigawa; wasu da nufin a yi gyara, wasu kuma na manufa ta tazarci, duk muna gode musu domin sun hasko wata fitila mai haske da za ta hasko halin da ilimi ya shiga  a jihar Jigawa daga 2015 zuwa 2023.

A ranar 09/04/2025 mai girma gwamnan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi ya ziyarci ofishin shugabar hukumar ilimin bai ɗaya ta ƙasa (UBEC), Dr. Aisha Garba domin tattauna muhimman abubuwan da suka shafi ilimin firamare a jihar Jigawa.

Bayan bayyana halin da ya tsinci ilimin a Jigawa da kuma nasarorin da aka samu, ya yi jawabi kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen haɗaka da jihar Jigawa ke bayarwa wajen yin gine-gine masu yawa da ba a buƙatarsu a musamman duba da yadda bukatar malamai ta fi buƙatar gina ajujuwa a wancan lokacin.

Gwamna Namadi ya buƙaci da hukumar ta UBEC ɗin, ta fifita amfani da kuɗaɗen hadakar wajen kula da makarantun da aka gina ba ƙirƙirar wasu ba; domin gina makarantun a guraben da ba a buƙata ya na janyo lalacewarsu da kuma laƙume maƙudan kudade wajen gyaran su, kuma jiha ce ke ɗaukar nauyi a lalitarta. Domin an yi amfani da kuɗaɗen al'umma wajen gina makarantu masu tarin yawa a guraben da aka fi buƙatar yawaitar malamai maimakon ajujuwa, an bayar da kwangilolin ginin makarantu masu yawa a guraben da babu daliban, an gina ajujuwa da suka fi karfin bukatun wasu makarantun da ke fama da ƙarancin malamai. An yi gine-gine masu yawa a gwamnatin baya,  ba tare da duba alfanun gine-ginen ba.

Har ila yau, gwamna ya bayyana irin nasarorin da gwnanatinsa ta samu wajen babban yunkuri na cike giɓin malamai a kan kowane dalibi a jihar Jigawa (Teacher gap) ta hayar ɗaukar malamai kusan 7,000. Ya kuma bayyana shirin horas da malamai 17,000 da aka yi.

Ya kara da bayyana yarjejeniyar da gwamnatin jihar Jigawan ta shiga da NEW GLOBE wajen sauya fasalin ilimin firamare a jihar Jigawa karkarshin shirin JigawaUNITE na sama da Bilyan 60, wadda za a yi amfani da fasahar zamani wajen koyar wa. Wannan ya biyo bayan rahotannin da gwamnan ya karba daga hukumomi da dama kan halin da ilimin firamare ke ciki a jihar Jigawa musamman a fannin kwazon yara. Ta yadda yara da dama ba sa iya rubutu da karatu yadda ya kamata.

KAN LALACEWAR GININ MAKARANTU...👇

Babban dalilin da ya kawo yawaitar lalacewa da rushewar ginin wasu daga cikin makarantun da ake gani ana ɗorawa a a social media shi ne yadda aka gina makarantun da ajujuwa a guraben da ba a buƙatarsu. Garuruwan da bai wuce a haɗe su a yi makaranta guda ba saboda karancin dalibai, sai a ce ko ina sai an gina makarantu. Guraben da ajujuwan da su ke da su sun wadata, sai an kara gina wasu "blocks" ɗin alhali kuma ba su ne abin da aka fi buƙata ba. Hakan ta sa ba a amfani da su, rashin amfani da su ya kawo yawaitar lalacewarsu da kuma rashin ingancin ginin. Wannan ta sa duk guraben da za ka ga ajujuwa sun lalace, za ka iske ba ajujuwan da ake amfani da su ba ne, wani sashe ne daga cikin makarantar musamman waɗanda aka gina babu buƙatarsu. Irin wannan gine-gine marasa amfani na daga cikin ayyukan da malam ya gada daga gwamnatin da ta gabata.

MATAKAN DA GWAMNA YA ƊAUKA👇

-Daga cikin abubuwan da malam ya gada akwai lalatattun makarantu da iskar da ruwan sama suka lalata, ya kuma ware maƙudan kudade domin gyara wadannan makarantu da suka lalace a cikin ƙwarya-ƙwaryar kasafin kudin shekarar 2023 da ya fara yi. Sannan an saka gyaran makaranta masu yawa, kewaye makarantu da dama sayo kujerun zama kimanin 1,300.

-Neman sauya fasalin yadda yarjejeniyar kudin haɗaka (SUBEB/UBEC matching funding) wadda da shi ne ake gine-ginen makarantu. Gwamna ya nemi da hukumar da ta mayar da hankali wajen amfani da wannan kudade wajen gyara tare da kula da makarantu da aka gina masu tarin yawa maimakon ci gaba da gina wasu. Domin ana barin gwamnatin jiha ne da kashe makudan kuɗaɗe wajen gyara wadannan makarantu da aka gina su a guraben da babu buƙatarsu.

-A sanya kuɗaɗen mai yawa a fannin ilimi cikin kasafin kudin wannan shekarar, wadda zai bayar da dama wajen yin gyare-gyare masu inganci domin ci gaba da ayyukan farfaɗo da ilimi a kowane fanni a jihar Jigawa.

© Al-Hadejawy 

@highlight

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)