Mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA ya jagoranci kafa harsashin gina gidaje 1,500 a fadin jihar Jigawa.
Gidajen waɗanda za a samar da su domin al'umma masu karamin karfi a kan farashi mai rahusa, an kirkire su ne domin magance matsalolin gidaje musamman ga ƙananan ma'aikata a jihar Jigawa.
Idan ba a manta ba, majalissar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da gina wadannan gidaje a karshen shekarar da ta gabata. Za a fara kashin farko na gine-ginen a kan N5,984, 880, 883.30k a helkwatar masarautu guda biyar da ke jihar Jigawa tare da wasu ƙananan hukumomi guda 3 wadanda su ke da manyan makarantu.
Dutse 600
Hadejia. 200
Gumel 100
Ringim 100
Kazaure 100
Birnin Kudu 100
Babura 150
Kafin 150
Taron ya samu halartar manyan-manyan baƙi daga ciki da wajen jihar Jigawa. Babban bako na musamman a wajen wannan taro shi ne Babban ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, mataimakin gwamnan jihar Jigawa; Engr. Aminu Usman Gumel, kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa Rt. Honourable Haruna Aliyu Dangyatin, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa; Alhaji Sani Isyaku Gumel, shugaban Jam'iyyar APC na jihar Jigawa, Alhaji Aminu Sani, shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar Jigawa, mai martaba sarkin Dutse; Alhaji Hamim Nuhu Muhammad Sunusi; kwamashinoni, Shugabannin ƙananna hukumomi, manya-manyan ma'aikatu da ƙananan hukumomi.
-Mallam Garba Al-Hadejawy FCAI, FIMC
Mataimaki na musamman ga mai girma gwamnan jihar Jigawa a fannin sabbin kafafen sada zumunta.
20 ga watan Janairu na shekarar 2024