Gwamnatin Jihar Katsina zata yi koyi da Jihar Jigawa wajen kafa kantin sauki (Palliative Shop)

Jigawa New Media Office
0

Gwamnan jihar Katsina Mai girma Dikko Umar Radda PhD ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci kantin sauki na gwamnatin jihar jigawa a garin Dutse.

Gwamna Radda yazo Jihar Jigawa ne domin halartar taron bude cibiyar addinin musulunci da masallacin Jama'a ta Alham (Alham Islamic Foundation) a garin Jahun. Cibiyar wani bawan Allah ne ya gina ta domin yada ilmin addinin musulunci. 

Gwamnan jihar Katsinan ya fara kaiwa mai girma gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ziyara a fadar gwamnatin jiha dake Dutse. Daga nan aka rankaya zuwa garin Jahun domin bude cibiyar.

Gwamnonin sun samu rakiyar Mataimakin gwamnan jihar jigawa Engr. Aminu Usman Gumel da shugaban majalisar jihar jigawa Rt. Honourable Haruna Aliyu Dangyatin, Kwamishinoni, masu rike da mukaman siyasa da manyan jami'an gwamnati. 
Bayan dawowa daga Jahun ne, aka zarce kantin sauki domin ganin yadda ake aiwatar da ahi.

Gwamna Radda ya yaba da hangen nesa na gwamna Namadi wajen bude wannan kanti don taimaka ma jama'a musamman a wannan lokaci na matsalar tattalin arziki.

Gwamna Radda yace nan gaba kadan jami'an gwamnatin jihar Katsina zasu zo Jigawa domin nazarin yadda ake gudanar da kantin sauki domin ganin sun samar da shi a jihar Katsina.

Gwamna Radda ya kuma yabawa Gwamna Malam Umar Namadi wajen baima noma muhimmaci, inda ya nemi sauran gwamnonin arewa maso yamma dasu yi koyi da Mai girma gwamna Malam Umar Namadi wajen bada kulawa ta musamman akan harkar noma.

Tuni dai Gwamna Radda ya koma gida Katsina.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)